Masu binciken sun ce akwai kara mai kama da fashewar bom da aka ji daga na’urar da ke nadar bayanai a jirgin.
Jirgin dai ya tarwatse ne bayan tashinsa minti 23 daga tashar Sharm al Sheikh a Masar a ranar Asabar karshen makon jiya. Kuma tuni mayakan IS da ke da’awar jihadi suka yi ikirarin daukar alhakin tarwatsewar jirgin.
Hasashen da ake bom ne ya tarwatse jirgin, ya sa baki ‘yan yawon bude na gaggawar ficewa Masar. 289